IQNA

UNESCO Ta Yi Gargadi Dangane Da Yiwuwar Hare-Haren Daesh A Wuraren Tarihi Na Syria

22:59 - September 17, 2015
Lambar Labari: 3364515
Bangaren kasa da kasa, hukumar adana kayan tarihi ta majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa akwai alamun da ke nuni da cewa yan ta’addan daesh na shirin kaddamar da hari kan wuraren tarihi na kasar Syria.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na PressTV cewa, shugabar hukumar UNESCO ta bayyana cewa bisa wasu hotuna da aka dauka ta hanyar tauraron dana dam an gano cewa yan ta’addan daesh na gina ramuka da ke nufin rusa wuraren tarihi nna Syria.

Mahkuntan kasar Syria sun ce ‘yan ta’adan IS sun kashe mutane da dama a tsohon birnin Palmyra dake tsakiyar kasar. Bayanai sun nuna cewa  akalla fararen hula dari hudu ‘yan ta’adan suka kashe a birnin na Palmyra, da suka hada  da mata da yara, bisa dalilin goyon bayan su ga shugaban kasar.

Da kuma kin karbar umurni daga kungiyar ta daesh, cikin wadanda suka rasa rayukan su akwai ma'aikatan hukumomi, da na kamfanonin gwamnatin, kana akwai mutane fiye da dubu daya, wadanda kungiyar ta hana fito daga birnin na Palmyra.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta kwace iko da garin palmyra mai tarihi a kasar Syria, kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kutsa cikin birni da ke tsakiyar kasar Syria, bayan da sojojin Syria su ka janye daga cikinsa.

Cibiyar kare hakkin bil’adama na kasar Syria, ta bakin shugabansa ya bayyana cewa kungiyar Is ta mamaye kusan dukkanin birnin sai dai ba ta shiga yankin da kurkuku da kuma hukumar leken asirin soja su ke ba a yammacin birnin saboda akwai sojoji masu a cikinsu.

Yankin ya kasance daya daga cikin tsofaffin daulolin da aka yi  gabanin haihuwar annabi Isa da daruruwan shekaru wacce kuma ta yi  gogayya da saular romawa.

3364448

Abubuwan Da Ya Shafa: unesco
captcha