IQNA

Ayatollah Sisitani Ya Yi Allah Wadai Da Shelanta Quds A Matsayin Birnin Isra’ila Da Trump Ya Yi

22:44 - December 07, 2017
Lambar Labari: 3482175
Bangaren kasa da kasa, babban malmin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya yi Allawadai da matakin Trump na  amincewa da birnin Quds a matsayin babban birnin Isra’ila.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ofishin babban malmin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani cwa, babban malamin ya yi Allawadai da amincewa da birnin Quds a matsayin babban birnin Isra’ila da Donald Trump na Amurka ya yi.

Bayanin ya ce, Allah Sistan ya bayyana matakin na Trump da cewa, ya bakanta zukatan daruruwan miliyoyin musulmi a fadin duniya, kuma birnin Quds birni ne na al’ummar Palastinu da yahudawan sahyuniya ‘yan mamaya suka mamaye.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana birnin quds a matsayin babban birnin gwamnatin yahudawan Isra’ila, tare da bayyana cewa za su fara shirin dauke ofishin jakadancin Amrka zuwa irnin.

Wannan mataki dai ya jawo fushin al’ummomin da dama, musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

3670438

 

 

 

 

captcha