IQNA

Putin Ya Gana Da Assad A Latakia Ta Syria

16:57 - December 11, 2017
Lambar Labari: 3482191
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci sojojin kasar su fara janyewa daga kasar Siriya zuwa gida.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban ya bayyana haka ne a safiyar yau Litinin a lokacin da ya kai ziyarar ba zata, zuwa sansanin sojojin kasar ta Rasha na Hmeymim  da ke birnin Latakia na kasar Siriya. 

Putin ya kara da cewa sojojin kasarsa sun cimma manufofinsu na wargaza kungiyar 'yan ta'adda da ke kiran kanta "daular musulunci" wato kungiyar Daesh a cikin shekaru biyu da suka gabata,

Shugaban na Rasha ya gana da takwaransa na kasar Siriya a wannan ziyarar ya kuma yi jawabi wa sojojin kasar ta Rasha da ke kasar ta Siriya kafin ya wuce zuwa kasar Masar. 

Rasha ta fara kai hare-hare kan mayakan kungiyar yan ta'adda ta Daesh ne a shekara ta dubu biyu da sha biyar.

3671589

 

 

captcha