IQNA

An Kawo Karshen Taron Gidajen Radiyon Kur'ani Na Duniya A Alkahira

23:47 - January 31, 2018
Lambar Labari: 3482352
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen babban taron kasa da kasa na gidajen radiyon kur'ani da aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yaum sabi cewa, a jiya an kawo karshen babban taron kasa da kasa na gidajen radiyon kur'ani da aka gudanar a birnin Alkahira.

Wannan taro ya kwashe kwanaki uku a jere ana gudanar da shi, tare da halartar jami'ai na gwamnati gami da malamai da kuma baki daga kasashen duniya daban-daban.

Taron ya mayar da hankali kan yadda za a karfafa batun wayar da kan msuulmi kan hakikanin koyarwar muslucni, ta yadda za a dakile yaduwar tsatsauran ra'ayin addinia  tsakanin musulmi musamman ma matasa, wanda hakan kan kai su zuwa ga shiga kungiyoyin 'yan ta'adda da sunan jihadi.

An gabatar da kasidu da bayanai masu tasiri, ta yadda gidajen radiyon musulmi da kuma sauran kafofin yada labarai za su mayar da hankali wajen fadakarwa ta hanyoyi na hikima masu jan hankali.

Minista mai kula da harkokin addini na kasar Masar ya gabatar da jawabinsa da ke jaddada wajabcin jawo matasa musulmi a jiki, maimakon nuna musu halin ko in kula, domin hakan zai haifar da dayan biyu, ko dai su koma masu bin aladun turai, ko kuma shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.

3687058

 

 

captcha