IQNA

A Gobe Za A Fara Zaman Makokin Shahadar Zahra (SA) A Stockholm Na Sweeden

22:16 - February 19, 2018
Lambar Labari: 3482410
Bangaren kasa da kasa,a gobe ne idan Allah ya kai mu za a fara zaman makoki na shahadar Sayyida Zahra a cibiyar Imam Ali (AS) da ke Stockholm babban birnin Sweeden.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar Imam Ali (AS) cewa, za a fara gudanar da wannan zaman ne daga gobe 20 ga watan Fabrairu.

Hottatol Islam Said Jazari shi ne zai gabatar da jawabi a wurin zaman makokin.

Babban abin da wannan taron makoki zai mayar da hankali a kansa shi ne, irin gudunmawar da wannan baiwar Allah ta bayar wajen gina al'umma mumina a kan tarbiya irin ta manzon Allah, hakuri da juriya irin na manzon Allah.

Irin tarbiya da kyawawan halaye na Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta, shi ne irin tarbiya da dukkanin limaman tsira na Ahlul bait (AS) suka tashi a cikinta.

Kamar yadda kuma ta zama babban abin buga misali a wajen gwarzantaka da nuna jajircewa wajen bin uamrnin Allah da manzonsa komai tsanani komai wahala ba tare da nuna karaya ba.

3692918

 

 

 

 

captcha