IQNA

Za A Fara Gwada Aiki Da Bankin Musulunci A Rasha

22:28 - February 22, 2018
Lambar Labari: 3482419
Bangaren kasa da kasa, za a fara gwada yin aiki da tsarin bankin musulunci a kasar Rasha.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni sun tabbatar da cewa, manyan bankunan kasar Rasha na Sberbank da kuma babban bankin kasar ne za su shiga gaba wajen fara gwada wannan tsari.

Yanzu haka an cimma yarjejeniya tare da bankin musulunci da kuma wadannan manyan banuka na kasar Rasha kan yadda za a fara aiwatar da shirin, da kuma bangarorin da za a fara gudanar da shi.

A ranar 27 ga wannan wata na Fabarairu ne dai dukkanin bangarorin za su gudanar da zama na musamman domin tattauna wannan batu, da kuma sanin daga inda za a fara.

3693742

 

 

 

 

 

 

 

captcha