IQNA

An fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Karo Na 32 A Najeriya

22:36 - February 24, 2018
Lambar Labari: 3482424
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki kao na talatin da biyu a jahar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Juma’a an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki kao na talatin da biyu a jahar Katsina tare da halartar makaranta 256 daga jahohi 32 na kasar gami da Abuja fadar mulki.

Musa Abubakar mamba a kwamitin gasar kur’ani ta kasa ya bayyana cewa, babbar manufar gudanar da gasar dai ita ce kara raya sha’anin kur’ani mai tsarki a tsakanin al’ummar musulmi na kasar.

Ya ce daga cikin kyautukan da za a bayar har da babur mai taya uku da kuma babur mai taya biyu, gami da kudade.

Abubakar ya kara da cewa wakilai daga ofisoshin jakadancin kasashe 18 ne za su halarci wurin gudanar da gasar.

3693953

 

 

captcha