Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria cewa, sheikh Nabil Qawuq mamba a majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah ya bayyana shiru da kasashen duniya da na larabawa suka yi kan ta’addancin da ‘yan ta’addan wahabiyawan takfiriyya suke aikatawa a Syria, ya bayyana irin goyon bayan da ‘yan ta’adda suke samu daga wadannan kasashe.
Ya ce ko shakka babu a duk lokacin da kasashen duniya masu girman kai na yahudawa suke son cimma wani buri a kan Syria ko kawayenta, sukan yi amfani da karnukan farautarsu daga cikin larabawa domin kara karfafa ‘yan ta’adda da makamai da kuaden man fetur da suke sayarwa, domin zafafa hare-hare a kan biranen Syria, domin yin amfani da hakan wajen cimma wani burin a siyasa akan gwamnatin Syria ko kuma kawayenta.