IQNA

Iran Ta Ce Amurka Ce Ummul Haba'isin Tabarbarewar Yarjejeniyar Nukiliya

16:17 - November 09, 2021
Lambar Labari: 3486533
Tehran (IQNA) Iran ta zargi Amurka da haifar da yanayin da ya sanya yarjejeniyar nukiliya a cikin wani hali.

Kasashen Jamus da Iran, sun tattauna game da batun yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar dubu biyu da sha biyar.

Yayin tattaunawar da ta wakana ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdollahian da takwaransa na Jamus, Heiko Maas a ranar Litini, sun jadadda wajabcin yin tattaunawa mai amfani, a tattaunawar da za’ayi nan gaba ta neman farfado da yarjejeniyar shekara ta tadubu biyu da sha biyar.

Tattaunawar za ta maida hankali ne kan dagewa Iran jerin takunkuman da Amurka ta kakaba mata tun bayan da tsohon shugaban aksar Donald Trump, ya yi, gaban kansa ya fice daga yarjejeniyar a cikin shekarar dubu biyu da sha takwas.

A ranar 29 ga watan Nuwamba nan ne ake sa ran kasashen da suka rage a yarjejeniyar da kuma Iran, zasu komawa bakin tattaunawa a Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar ta shekarar dubu biyu da sha biyar.

 

4011856

 

captcha