IQNA

Fitattun 'yan Siyasa Musulmi A Amurka Sun Mara Wa Biden Baya

21:36 - July 21, 2020
Lambar Labari: 3485006
Tehran (IQNA) 'yan siyasa musulmi sun goyi bayan Joe Biden yayin da shi ya yi alkawalin cewa zai soke dokar hana musulmi daga wasu kasashe shiga Amurka idan har ya lahe.

Kamfanindillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, Dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya halarci wani taron musulmi da aka gudanar ta yanar gizo, wanda kungiyar Emgage Action ta dauki nauyin shiryawa kan yadda musulmi za su kada kuri’a, wanda aka gudanar kai tsaye ta hanyar yanar gizo, wanda kuma Joe Biden yana daga cikin wadanda kungiyar musulmin ta gayyata.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Joe Biden ya bayyana cewa, kuri’ar musulmi miliyan daya tana da muhimmanci a wurinsa, a kan haka yana da bukatar kuri’u na dukkanin musulmi da suke cikin Amurka, kamar yadda kuma ya yi alkawalin cewa zai soke dokar da Trump ya kafa ta hana musulmi daga wasu kasashe shiga cikin Amurka.

Haka nan kuma Joe Biden ya bayyana Donald Trump da cewa yana a matsayin munkari ne, wanda manzon Allah Muhammad ya ce a kawar dad a hanu, ko da harshe ko kuma da zuciya, wanda shi ne mafi raunin imani, inda ya ce musulmi za su iya bayar da gudunmawa wajen kawar da Trump da kuri’unsu a lokacin zabe.

 

3911632

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gudunmawa dan takarar
captcha