IQNA

Rauhani: Sabuwar Shawarar Amurka Ta Yi Hannun Riga Da Kudirin Yarjejeniyar Nukiliya

20:12 - August 13, 2020
Lambar Labari: 3485080
Tehran (IQNA) Rauhani ya bayyana cewa, ya kamata kasashe mambobi a kwamitin tsaro  su yi aiki da kudiri mai lamba 2231 wanda ya wajabta cire wa Iran takunkumin saye da sayar da makamai.

A wata tattaunawa da suka yi a yammacin yau ta wayar tarho, shugabannin kasashen Iran da Faransa sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, da kuma wasu batutuwa na kasa da kasa.

Shafin yanar gizo na fadar shugaban kasan kasar Iran ya sanar da cewa,a yau shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tuntubi shugaba Rauhani na Iran ta wayar tarho, inda suka tattauna a kan muhimamn lamurra da suka shafi gabas ta tsakiya da kuma wasu batutuwa na kasa da kasa.

Bayanin ya ce; Rauhani da Macron sun tattauna kan batun halin da ake ciki a kasar Lebanon, bayanan kuma sun tattauna batun yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, kamar yadda kuma suka tattauna hanyar hada-hadar kudade ta Instex tsakanin Iran da kasashen tarayyar turai.

Dangane da batun daftarin kudirin da Amurka ta gabatarwa mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin sabunta takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai kuwa, Rauhani ya ce da Macron, ya kamata kasashe mambobi a kwamitin su yi aiki da dokokin kasa da kasa, ta hanyar yin aiki da kudiri mai lamba 2231 wanda ya wajabta cire wanann takunkumi a ranar sha takwas ga watan Oktoban wanann shekara, tare da yin watsi da sabon daftarin kudirin na Amurka.

Haka nan kuma Rauhani ya kara da cewa, ya kamata kasashen da ke cikin tarayyar turai su zama masu ‘yancin siyasa saboda maslaharsu da al’ummominsu, maimakon bin Amurka ido rufe.

 

 

3916319

 

captcha