IQNA

Sojojin Hayar Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula A Yemen

23:37 - October 01, 2020
1
Lambar Labari: 3485235
Tehran (IQNA) Sojojin hayar gwamnatin Saudiyya sun kashe mata biyu fararen hula hula a cikin lardin Al-daidah na kasar Yemen tare da jikkata wasu.

Tashar talabijin ta Almasirah ta bayar da rahoto daga birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen cewa, a daren jiya mayakan haya na gwamnatin Saudiyay sun harba makaman atilare a kan kauyen Al-rabsa da ke cikin gundumar Hudaida, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mata biyu da kuma jikkatar wasu.

Wadannan hare-haren dai na zuwa kokarin da Saudiyya take yi tare da taimakon Amurka da wasu kasashen turai, domin mamaye lardin Al-hudaida mai matukar muhimamnci a kasar Yemen.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata Saudiyya ta kashe fararen hula a cikin kauyukan Shajin, Al-Munqim da kuma Duraihami da ke cikin gundumar ta Al-hudaidai a yammacin kasar Yemen.

 

3926575

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Zakariyya abubakar danbaba
1
1
Saudiyya kiyitunani wataranafa turawa kankizasudawu
Kekuma
captcha