IQNA

Fiye Da Mutane Miliyan 14 Da Dubu 500 Ne Suka Taru A Taron Arbaeen Na Bana A Karbala

22:16 - October 08, 2020
Lambar Labari: 3485257
Tehran (IQNA) fiye da masu ziyara miliyan 14 da dubu 500 ne suka taru a yau a taron arbaeen a birnin Karbala na Iraki.

Miliyoyin mabiya mazhabar ahlul bait suna gudanar da tarukan arbaeen a sassa daban-daban na duniya, domin tunawa da cikar kwanaki 40 bayan kisan gillar da aka yi Imam Hussain (AS) jikan manzon Allah a raar 10 ga watan Muharram.

Wannan taro dai an jima ana gudanar da shi a tarihi, inda jama’a kan taru a hubbaren Imam Hussain (AS) da birnin Karbala na kasar Iraki, domin halartar karatun addu’oin ziyara, da kuma sauraren jawabai da ake gabatarwa.

A wannan shekara ma ana gudanar da irin wannan taro, duk kuwa da cewa a shekarar bana an dauki kwararan matakai na takaita yawan masu halartar taron, sabanin shekarun da suka shude, inda wasu lokutan adadin masu halartar taron kan kai mutane sama da miliyan sha takwas zuwa ashirin.

Baya ga kasar Iraki ana gudanar da wadannan taruka a wasu kasashe a yankin gabas ta tsakiya, da kuma Asia, gami da kasashen turai da na Afirka har ma da Amurka, inda manufar gudanar da taron daya ce, wato tunawa da abin da ya faru da zuriyar manzon Allah a irin wannan lokaci.

A kasar Iran an gudanar da taron tare da halartar jagora a Husainiyar Imam Khomenei da ke birnin Tehran, tare da halattar jagoran juyin juya halin muslunci na kasar.

 

3928156

 

 

 

captcha