IQNA

A Kullum Rana Akalla Mutane 25 Ke Mutuwa Sakamakon Rufe Filin Jirgin San’a Yemen

23:55 - October 13, 2020
Lambar Labari: 3485272
Tehran (IQNA) a kowace rana akalla mutane 25 ne suke mutuwa sakamakon ci gaba da rufe filin jirgi na San’a a Yemen

Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa Khalid Shaif babban daraktan filin jirgi na birnin San’a a Yemen ya bayyana cewa,  a kowace rana akalla mutane 25 ne suke mutuwa sakamakon ci gaba da rufe wannan filin jirgi.

Babban daraktan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da tashar talabijin ta almasirah, inda ya bayyana cewa, yanzu haka akwai mutane 30 daga cikin wadanda aka yi wa magani a kasar Jordan da suke son dawowa gida, amma babu damar hakan, sabod filin jirgin baya aiki.

Ya ci gaba da cewa, majalisar dinkin duniya da sauran bangarori na kasa da kasa ba da gaske suke yi ba kan batun dakatar da 'yan mamaya daga hare-haren da suke kaddamarwa kan al'ummar kasar tare da yi musu kisan gilla.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, yanzu haka akwai mutane fiye da dubu 30 da suke cikin jira domin fitar da su waje domin yi musu magani, sakamakon raunukan da suka samu, a hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar.

 

3929146

 

 

captcha