IQNA

Rauhani: Nan Da Lahadi Mai Zuwa Za A Janye Takunkumin MDD Na Hana Iran Saye da Sayar Da Makamai

23:53 - October 14, 2020
Lambar Labari: 3485273
Tehran (IQNA) shugaban kasar Iran ya bayyana cewa nan da ranar Lahadi Amurka za ta kara shan wata kunya dangane da kasar Iran.

Shugaba Dr. Hassan Rauhani wanda ya ke Magana a wurin taron majalisar ministoci da safiyar yau Laraba ya ci gaba da cewa; A cikin shekaru 4 na bayan nan Amurka ta bude wani sabon rikici da Iran akan wannan batu, sai dai a cikin wannan lokacin Amurkan ta ci kasa wajen samun goyon baya domin ci gaba da aiki da takukunmin hana saye da sayar da makaman akan Iran.

Dr. Rauhani ya ci gaba da cewa; An sami wannan nasarar ce saboda kokarin diplomasiyyar Iran, sannan ya kara da cewa; Dauke wa Iran din takunkumin daya ne daga cikin sakamakon yarjejeniyar Nukiliyar Iran, don haka daga ranar Lahadi mai zuwa za mu iya saye da kuma sayar da makamai ga kowace kasa a duniya.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma siffata mazauna fadar mulkin Amurka ta “White House” da cewa ashararai ne

Shugaban na kasar Iran ya ci gaba da cewa; Muna ganin yadda ashararancin Amurka bai tsaya akan Iran kadai ba, ya shafi al’ummu da dama da suka hada da Afghanistan, inda kullum su ke cewa za su tabbatar da tsaro amma hakan ba ta faru ba.

Har ila yau, shugaban kasar na Iran ya yi ishara da Amurka da ta riya cewa za ta yi maganin Da’esh a Iraki da Syria, ba ta yi ba, alummun wadannan kasashen ne da kuma taimakon Iran su ka kawo karshen ‘yan ta’addar.

https://iqna.ir/fa/news/3929244

captcha