IQNA

Lavrov Ya Ce Kulla Alaka Tsakanin Larabawa Da Isra’ila Bai Kamata Ya Cutar Da Falastinawa Ba

23:56 - October 14, 2020
Lambar Labari: 3485274
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, bai kamata kulla duk wata alaka tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila ya cutar da Falastinawa ba.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake zantawa da tashar rediyon kasar Rasha a birnin Moscow, mi Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, Rasha ba ta da matsala kan kulla alaka tsakanin kasashen larabawa da Isr’ila, amma da sharadin cewa hakan ba zai cutar da al’ummar Falastinu ba.

Ya ci gaba da cewa, suna girmama duk duk wani shiri na diflomasiyya tsakanin Isra’ila da wata kasa, amma idan bai yi hannuun riga da ka’idoji da dokokin da majalisar dinkin duniya ta shata ba.

 

3929376

 

 

captcha