IQNA

An Tayar Da Gobara a Cikin Asibitocin Tafi Da Gidanka Na Hashd Sha’abi A Iraki

23:57 - October 14, 2020
Lambar Labari: 3485275
Tehtan (IQNA)  wasu wadanda ba a san ko su wane na ba sun kunna wuta a cikin asibitocin tafi da gidanka ta Hashd Sha’abi a Najaf.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu wadanda ba a san ko su wane na ba sun saka wuta wadda ta jawo gobara a cikin asibitocin tafi da gidanka guda biyu na rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hashd Sha’abi, a birnin Najaf da ke kudancin kasar.

Rahoon ya ce, rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hashd Sha’abi ta kafa wadannan asibitocin ne domin bayar da taimakon gaggawa ga jama’a masu ziyarar arba’in.

An kunna wutar ne da gangan, kuma hakan ya yi sanadiyyar konewar dukkanin kayan aiki da ke cikin wadannan asibitoci, da kuma tarin magunguna da aka tanada domin hidima ga jama’a.

Jami’an tsaro dai sun shiga gudanar da bincike kan faruwar lamarin, da zimmar ganin an kame duk wadanda suke da hannu a cikin lamarin.

3929247

 

captcha