IQNA

An Kara Yawan Na’urori Masu Aikin Feshin Maganin Kashe Cutuka A Masallacin Haramin Makka

23:46 - October 15, 2020
Lambar Labari: 3485277
Tehran (IQNA) an kara yawan na’urori masu aikin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin masallacin hramin Makka.

Tashar arab news ta bayar da rahoton cewa, Hassan Al-suwairi daya daga cikin manyan jami’ai masu kula da lamarin kiwon lafiya a masallacin harami da na manzo ya bayyana cewa, an kara yawan na’urori masu aikin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin masallacin hramin Ka’aba mai alfarma.

Ya ce an dauki wannan matakin ne domin kara tabatar da cewa ana kiyaye lafiyar jama’a da suke gudamar da ayyukan ibada da ziyara a masallacin hrami da kuma masallacin manzo da ke Madina.

Haka na kuma ya yi ishara ga wasu matakan na daban da ake dauka, domin tabbatar da cewa an dakile yaduwar cutar korona a tsakanin masu gudanar da ayyukan ziyara a wadannan wurare masu tsarki, wadanda za su taimaka wajen samun natsuwa a yayin ayyukan hajji ko Umra.

 

3929446

 

  

captcha