IQNA

Musayar Fursunoni Tsakanin Gwamnatin San’a Yemen Da Da Masu Yaki Da Kasar

23:55 - October 15, 2020
Lambar Labari: 3485278
Tehran (IQNA) Ansarullah ta sako wasu Amurkawa biyu da take tsare da su domin ba da damar dawowar wasu ‘yan kasar Yemen sama da dari biyu da suke kasar Oman.

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sako wasu Amurkawa guda biyu da take tsare da su don ba da damar dawowar wasu ‘yan kasar Yemen sama da dari biyu da suke kasar Oman wadanda suka gagara dawowa gida saboda killacewar da Saudiyya da kawayenta suka yi wa kasar Yemen din.

Rahotanni sun ce a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne dai aka cimma yarjejeniyar musayen wanda kasar Oman ta taka rawa wajen cimma shi tsakanin ‘yan kungiyar Ansarullah din da Saudiyya da Amurkawan.

Wani mai taimakawa shugaban Amurkan Donald Trump, Kash Patel, ya bayyana cewar Amurkawan da aka sako din su ne Sandra Loli, wata ‘yar agaji da ake tsare da ita na kimanin shekaru uku a Yemen din da kuma Mikael Gidada, wani dan kasuwa da ake tsare da shi sama da shekara guda, sai kuma gawar wani Ba’Amurken mai suna Bilal Fateen, wanda tuni aka aika da ita zuwa Amurkan.

Shi ma a nasa bangaren kakakin kungiyar Ansarullah din Mohammad Abdulsalam ya tabbatar da sakin Amurkawan da kuma cewa tuni wadannan ‘yan kasar Yemen din sama da 240 suka isa birnin Sana’a, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun makale a Oman din ne bayan sun dawo daga shan magani sakamakon hare-haren wuce gona da irin Saudiyya, amma suka gagara dawowa gida saboda ci gaba da killace kasar Yemen din da Saudiyya da kawayenta suke yi.

 

3929473

 

captcha