IQNA

Iran: Jagora Ya Halarci Makoki Zagayowar Ranar Wafatin Manzon Allah (SAW)

23:46 - October 16, 2020
Lambar Labari: 3485279
Tehran (IQNA) A irin wannan ranar ce manzon Allah (saw) ya yi wafati, kamar yadda kuma a irin wannan ranar ce Imam Hassan Almujtaba (AS) ya yi shahada.

A Tehran dai jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Ali Khamenei ya halarci zaman makoki don aukuwar wadannan al-amura a husainiyyar Imam Khomaini (q) da ke cikin gidansa, amma ba tare da hallatar mutanen gari ba, saboda matsalar cutar korona wacce kasar take fama da ita. Amma an nuna zaman a gidajen talabijin na kasar kai tsaye.

Hajjatul Isalam Hamid Khashani ne ya gabatar da jawabi dangane da wannan musibar, sannan wani daga cikin masu karanta makokin ya karanta makokin da ya dace da hakan.

 

3929563

 

 

 

 

captcha