IQNA

Moscow: Matsaya Hizbullah Kan Batun Shata Iyakokin Lebanon Na Kan Doka

23:26 - October 17, 2020
Lambar Labari: 3485284
Tehran (IQNA) Rasha ta kare matsayar da Hizbullah ta dauka na kin amincewa da tsarin tawagar Lebanon da za ta tattauna kan shata iyaka da Israila.

Tashar almayadeen ta bayar da rahoton cewa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, abin da Hizbullah ta bayyana dangane da tawagar da Lebanon da za ta tattauna da Isra’ila gaskiya ne.

A cikin bayanin hadin gwiwa da kungiyoyin Hizbullah da Amal suka fitar, sun nuna rashin amincewarsu da yadda aka tsara tawagar da kasar Lebanon, wadda za ta tattauna da Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani, kan batun sake iyakokin ruwa na Lebanon da kuma Palestine da yahudawa suka mamaye.

A cikin bayanin kungiyoyin biyu sun bayyana cewa, wannan tattaunawa ta ginu ne bisa ga abin da aka cimma matsaya akansa wanda shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Birri ya sa hannu akansa, shi ne kan cewa tawagar Lebanon da za ta tattauna da Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani kan batun iyakoki, za ta kunshi jami’an soji da na tsaron kasar Lebanon kawai.

A cikin tawagar da aka kafa a halin yanzu, akwai fararen hula, wanda hakan ya saba wa abin da aka amince da shi a hukumancea  kasar ta Lebanon, wanda hakan ne yasa Hizbullah da Amal suka nuna rashin gamsuwarsu da tsarin tawagar, wanda kuma gwamnatin Rasha ta bayyana matsayin na Hizbullah da Amal da cewa yana kan doka.

3929513

 

captcha