IQNA

An Bude Masallacin Harami

Tehran (IQNA) an bude masallacin haramin ka'abah mai alfarma ga masu gudanar da ayyukan ibada na umrah, bayan kwashe tsawon watanni 7 wurin yana rufe, tare da daukar matakan takaita masu ziyara. Wadannan matakai har sun shafi masu gudanar da aikin hajji a shekarar bana, inda adadi kalilan suka gudanar da wannan aiki saboda matakan dakile yaduwar cutar corona. Akwai mutane 4,000 da suke yin aikin tsaftace wurin a kullum rana.
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: masallacin harami ، mai alfarma ، aikin Umrah ، hajji ، bana