Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da jam’iyyar ta “Alwifaq” ta fitar inda ta bayyana cewa; A ranar Lahadi sha takwas ga watan Oktoban wannan shekara tawagar ‘yan sahayoniya ta isa Bahrain a daidai lokacin da al’ummar suke cike da fushi, kuma mahukuntan kasar sun dauki tsauraran matakai na tsaro.
Bugu da kari sanarwar ta ci gaba da cewa; Mahukuntan kasar sun yi amfani da ‘yan bada domin hana al’ummar kasar bayyana fushinsu akan kulla alaka da ‘yan sahayoniyar.
Jam’iyyar ta “Alwifaq’ ta kara da cewa; Alakar da mahukuntan kasar su ka kulla da ‘yan sahayoniya ta sabawa doka, domin ba ta wakiltar al’ummar kasar da basu yarda da ‘yan sahayoniya barayin kasa ba.
Wani sashe na sanarwar ya kunshi cewa; Tabbas al’ummar kasar ta Bahrain za su ga bayan wannan haramtacciyar yarjejeniyar da ‘yan sahayoniya.