A cikin rahoton da ta bayar tashar almasirah ta bayyana cewa, a cikin wani jawabi da ya gabatar a yammacin yau Litinin, Sayyid Abdulmalik Alhuthi jagoran kungiyar Ansarullah, ya bayyana cewa; wasu daga cikin sarakuna da shugabannin larabawa maciya amanar al’ummominsu, suna ta hankoron ganin sun kulla hulda da yahudawan Isra’ila, domin farantawa iyayen gidansu da ke Amurka.
Haka nan kuma ya ce wadannan sarakuna da shugabannin larabawa ba su wakiltar al’ummominsu, kamar yadda kuma basu wakiltar al’ummomin musulmi, domin kuwa suna zartar da manufofin ‘yan mukin mallaka nea kasashen nasu, ta hanyar yin mulkin mulukiya da kama karya, ba bisa ra’ayin mutanensu ba.
Ya kuma yi ishara da yadda shugabannin Amurka da na Isra’ila suke son yin amfani da wannan batun domin cimma manufofinsu na siyasa, sakamakon bore da kakkausar suka suka daga suke fuskanta daga al'ummominsu.