IQNA

Muhimmiyar Gudunmawar Manzon Allah (SAW) Wajen Yaki Da Nuna Wariyar Launin Fata

16:20 - October 05, 2021
Lambar Labari: 3486388
Tehran (IQNA) Babban sakataren cibiyar nazari da bincike ta kasar Lebanon ya bayyana cewa Manzon Allah (SAW) ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaki da nuna bambanci da wariyar launin fata.

Hojjatoleslam "Sayyid Fadi Al-Sayyid" Babban Sakataren Cibiyar Nazari da bincike ta Lebanon, a yayin zagayowar lokacin tunawa da wafatin manzon Allah (SAW) a wata hira ta musamman da IQNA, domin bahasi kan halayensa a cikin ayoyin Alkur'ani mai tsarki ya yi bayanin abubuwan daban-daban.

IQNA: Wadanne abubuwa ne na musamman da sirar manzon Allah (SAW) ta kebanta da su?

Tarihin Annabi mai tsira da amincin Allah da alayensa yana da bangarori da dama da suka haɗa da duniya da lahira, musamman ɓangaren 'yan adamtaka; Domin shi ɗan adam ne kafin aikinsa, kuma wannan tabbataccen lamari ne na gaskiyarsa game da abin da aka aiko shi da shi na sako daga Allah.

Bugu da kari, kamala ta fuskoki daban-daban, da kyakkyawar zamantakewa tana daga cikin halayensa madaukaka; Domin ya kasance uba, kuma mai gida, sannan kuma jagora.

Kafin aiko shi, Manzon Allah (SAW) ya kasance a cikin mutanensa mutum ne mai kyawawan dabi'u da kyawawan halaye, ciki har da yin gaskiya da rikon amana; Wannan shi ne abin da Annabi (SAW) ya shahara da shi tun kafin aiko shi da sakon musulunci, kuma makiyansa ma sun shede shi da hakan.

Bayan aiko shi da sako kuma, abin da sakonsa ya kunsa shi ne tabbatar da kyawawan dabi'u da 'yan adamtaka da kuma kadaita Allah madaukakin sarki.

Abubuwa da dama sun faru a cikin tarihin ma'aiki da suke nuni da cewa, shi mutum ne da yake girmama dan adam, hatta wadanda suka cutar da shi, yana kyautata musu, duk da cewa cewa dama can bsa dabi'arsa shi mutum ne mai tsananin hakuri da juriya, amma kuma a lokaci guda, sakon da ya zo ya da shi daga Allah madaukakin sarki ya tabbatar da irin wadannan kyawawan halaye.

Manzon Allah (SAW) ya zama shi ne manzo kuma malami a lokaci guda wanda yake koyar da mutane kyawawan dabi'un Allah madauakki yake bukatar bayinsa su siffatu da su, kamar yadda dukkanin wadannan dabi'u suke a aikace a cikin ayyukan manzon Allah (SAW).

'Yan adamtaka irin ta manzon Allah ta tabbatar da cewa, sakon da ya zo da shi sako ne na shiriya ga dukkanin 'yan adam baki daya, ba na wata al'umma ko wata kabila ne ita kadai ba.

 

4002504

 

 

 

captcha