IQNA

Shugaba Assad Ya Soke Mukamin Babban Mufti A Syria Domin Karfafa Babban Kwamitin Malaman Fikihu Na Kasar

19:34 - November 16, 2021
Lambar Labari: 3486565
Tehran (IQNA) a kasar Syria Shugaba Bashar Al-Assad ya soke mukamin babban malamin addinin islama mai bayar da fatawa na kasa.

Shugaba Bashar Al-Assad na Siriya, ya soke mukamin babban malamin addinin islama mai bayar da fatawa a kasar wato mufti, wanda Sheikh Ahmad Badreddine Hassoun ke rike da tun cikin 2004.

Kamfanin dillancin labarai na Sana ya sanar a ranar Talata cewa, an soke mukamin babban Mufti na kasar wanda ke wakiltar babbar hukumar addinin Musulunci a kasar ta hanyar umarnin shugaba Bashar al-Assad.

Dakar, ta ce an aike da Sheikh Ahmad Badreddine Hassoun mai shekaru 72, zuwa ritaya, Inda aikinsa zai koma hannun majalisar shari'ar musulunci, hukumar dake karkashin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

Daga yanzu majalisarsa ce za ta rika tantance kalanda kuma ta kuma ba da ra'ayi kan harkokin addini, a kokarin da gwamnati ke yi na fadada sa ido kan al’amura na addini.

 

4013574

 

captcha