IQNA

Sabon Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Musulmi Dan Kasar Chadi Ya Fara Aiki A Ofishinsa A Yau

23:04 - November 17, 2021
Lambar Labari: 3486574
Tehran (IQNA) sabon babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya fara aiki a ofishinsa a yau.

Shafin yanar gizo na OIC ya bayar da bayanin cewa, a yau Hussein Ibrahim Taha ya fara aiki a matsayinsa na babban sakataren kungiyar kasashen musulmi a hukumance.

A zaman taro karo na arba'in da bakwai na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da aka gudanar a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, aka ayyana shi a matsayin sabon sakataren janar na kungiyar.

An haifi Hussein Ibrahim Taha a shekarar 1951 a birnin Abshi na kasar Chadi, inda ya yi karatun firamare da sakandare a kasar Chadi.

Baya ga aikin jakadanci da ba da shawara, an zabe shi a matsayin ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Chadi a shekarar 2017, kuma an nada shi mai baiwa shugaban kasa shawara a shekarar 2019.

Sauran mukaman nasa sun hada da jakadan Chadi a Faransa, Spain, Portugal, Girka da kuma Vatican. Ya kuma kasance babban mai ba da shawara ga ofishin jakadancin Chadi a Saudiyya.

Sabon Sakatare Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci, wanda ya kware a harsunan Faransanci, Larabci da Ingilishi, ya karbi sabon mukaminsa na Sakatare Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ne a matsayin magajin Yusuf bin Ahmad Al-Uthaymeen.
 

4014151

 

 

captcha