IQNA

Kungiyar Musulumi Mafi Girma A Arewacin Amurka Ta Shiga Cikin Masu Rajin Kare Muhalli

14:59 - November 20, 2021
Lambar Labari: 3486582
Tehran (IQNA) Kungiyar Islamic Association of North America (ISNA) ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar kare muhalli daga gurbata.

Shafin Geen Faith ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar ta Islamic Association of North America  ta rattaba hannu a kan wannan tare da yin kira ga sauran addinai da su fitar da sanarwar hadin gwiwa don nuna goyon baya ga yarjejeniyar.

A cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa dai hard a daukar matakai na kiyaye gurbatar muhalli ta fuskar hana zubar da abubuwa da za su iya kawo kawo gurbatarsa.

Haka ya hada da zubar da robobin da aka gama amfani da su, ko kuma gurbataccen mai, ko fitar da hayaki na ababen hawa masu matsala da makamantan hakan.

Kungiyar ta ce daukar wannan mataki na alaka ne da ‘yan adamtaka da kuma kare rayuwar bil adama da muhallainsu na rayuwa.

 

4014131

 

 

captcha