IQNA

Makarancin Kur'ani Mai Lakabin Farisul Qurra A kasar Masar

21:36 - November 21, 2021
Lambar Labari: 3486588
Tehran (IQNA) Sheikh "Ahmad Abu Fayyuz" fitaccen makaranci ne na kasar Masar daga lardin Kafr Sheikh, wanda aka fi sani da "Farisul Qurra" a kasar.

Sheikh "Ahmad Abu Fayouz" shi ne shugaban kungiyar makaranta ta lardin Kafar Sheikh, kuma daya daga cikin fitattun masu karanta kur'ani na zamani a kasar Masar, wanda ke karatun kur'ani a gidajen rediyo da talabijin na kasar.

Saboda kyakykyawan sautinsa da karatunsa mai karfin gaske ya sa ya shahara a wajen masoya Alkur'ani mai girma, kuma ana kiransa da "Faris al-Qurra" a kasar Masar.

An haifi Ahmad Awad Abu Fayouz a shekara ta 1978 a kauyen Abu Ziyadeh da ke gundumar Dasuk a lardin Kafr Sheikh a kasar Masar, kuma ya haddace kur'ani mai tsarki yana da shekaru tara.

Tun yana karami ya kasance yana halartar tarukan kur'ani mai tsarki domin sauraren karatun fitattun mahardata na kasarsa.

Yana da shekaru 15 a duniya ya shahara sosai a kauyukan da ke kusa da Desouk, bayan nan kuma shahararsa ta yadu zuwa garuruwan lardin Kafr Sheikh, har sai da ya shahara a wasu lardunan Masar saboda kyakykyawar muryarsa da kuma kwarewarsa wajen karanta Alqur'ani mai girma.

Kyakyawan sautin wannan makarancin dan kasar Masar ne ya sanya ya cinye  jarrabawar karatun kur'ani a gidan rediyo da talabijin na kasar Masar, kuma ya samu nasarar wannan jarabawar ta hanyar samun amincewar 'yan kwamiti, wanda ta haka ne a shekarar 2011 ya zama amintaccen makarancin gidan rediyo da talabijin na Masar.

 
آشنایی با «فارِس القراء» مصر + عکس
 
آشنایی با «فارِس القراء» مصر + عکس
 
آشنایی با «فارِس القراء» مصر + عکس
 
آشنایی با «فارِس القراء» مصر + عکس
 
آشنایی با «فارِس القراء» مصر + عکس

https://iqna.ir/fa/news/4014862

Abubuwan Da Ya Shafa: amincewa kwamiti
captcha