IQNA

Saudiyya Ta Kaddamar Da Munanen Hare-Hare A Kan Birnin San'a Na Kasar Yemen A Yammacin Yau

22:02 - November 25, 2021
Lambar Labari: 3486607
Tehran (IQNA) jiragen yakin gwamnatin kasar Saudiyya sun kaddamar da munanan hare-hare a kan birnin San'a fadar mulkin kasar Yemen a yammacin yau.

Tashar Almasirah daga birnin Sana'a fadar mulkin kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a yammacin yau Alhamis jiragen yakin gwamnatin kasar Saudiyya sun kaddamar da munanan hare-hare a kan yankuna daban-daban na birnin.

A cewar rahoton, baya ga birnin San'a, jiragen yakin masarautar Al Saud sun kai wasu hare-hare a wasu alrduna na kasar ta Yemen a yau, da suka hada da Hijjah da kuma Ma'arib.

Baya ga haka kuma jiragen na masarautar Al Saud sun kai wasu hare-hare a lardin Al-hudaidah, inda rahoton ya ce a cikin sa'oi 24 da suka gabata, Saudiyya ta kai hari sau 188 a cikin yankuna daban-daban ba lardin Alhudaidah.

Hare-Haren na masarautar Al Saud kan al'ummar kasar Yemen na zuwa na kwana daya bayan rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar, dangane da alkalumman mutanen da suka rasa rayukansu a Yemen sakamakon yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar a cikin shekaru bakawai.

 

https://iqna.ir/fa/news/4016128

captcha