IQNA

Baje Kolin Kasa Da Kasa Na Abincin Halal A Birnin Istanbul

20:38 - November 26, 2021
Lambar Labari: 3486609
Tehran (IQNA) an bude baje kolin kasa da kasa a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
A bisa rahoton kamfanin dillancin labaran Anatoly, a jiya Alhamis ne aka bude kasuwar baje kolin abincin halal a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya.
 
A taron na kasuwar baje kolin abincin Halal na Duniya karo na 7, wanda aka kwashe tsawon shekaru ana gudanar da shi amataki na kasa da kasa, a wannan karon baya ga baje samfurin abincin Halal daga kamfanoni daban-daban daga kasashen duniya, a gefe guda kuma za a tattauna batutuwan da suka shafi kasuwar Halal tare da halartar masana da jami'an siyasa da 'yan kasuwa daga Turkiyya da sauran kasashe.
 
A wannan shekara, ana gudanar da taron Halal na Duniya karo na 7 daga ranar 25 zuwa 28 ga Nuwamba 2021, a Cibiyar Taro ta Istanbul, taron na bana yana da taken "Sabon Zamani da Sabbin Ka'idoji Wajabcin Samar da abincin Halal".
 
An shirya taron na baje koli tare da hadin gwiwar cibiyar bunkasa harkokin kasuwanci ta Musulunci (ICDT) da kuma cibiyar kula da ka’idoji da yanayin kasashen musulmi (SMIIC). kamar yadda kuma baje kolin ya kunshi bangarori daban-daban na irin kayayyakin da ake nunawa na abincin da ya halasta ga musulmi.
 
Mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fouad Oktay ya bayyana a wajen bude taron cewa, girman tattalin arzikin duniya ya karu daga dala tiriliyan 4 a shekarar 2017 zuwa dala tiriliyan 7 a yanzu.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4016319
captcha