IQNA

Ayyukan Hadin Gwiwa Na Binciken Ilimin Kimiyya Tsakanin Iran Da Uganda

16:20 - November 27, 2021
Lambar Labari: 3486611
Tehran (IQNA) Mataimakin shugaban jami'ar muslunci ta Uganda ya ce za su yi kokari wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasar da kuma Iran musamman a fannin ayyukan hadin gwiwa na bincike ilimin kimiyya.

Karamin jakadan Iran a Uganda Mohammad Reza Ghezelsofli ya ce, Iran da Uganda suna gudanar da ayyuka tare domin karfafa dangantaka da bunkasa hadin gwiwar bincike a bangaren ilimin kimiyya, da al'adu.

Jami'in difomasiyyar na Iran ya bayyana hakan ne  yau a lokacin ganawa da wasu jami'ai a bangaren ma'aikatar ilimi ta kasar Uganda abirnin Kampala, inda Kasoussi Idrissa Sinani, mataimakin shugaban jami'ar IUIU ta Uganda da sauran kwalejojin da ke da alaka da su ya gabatar da bayani dangane da irin ci gaban da ake samu ta fuskacin ayyukan hadin gwiwa a tsakanin Uganda da Iran a bangarori na binciken ilimin kimiyya da fasaha.

Sinanani ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kasa ce mai ilimi da masana masu tarin yawa a bangaren kimiyya, da kuma fitattun mutane wadanda suka kware a fannin ilimin likitanci da magunguna da aikin injiniya, saboda haka Uganda za ta kara karfafa dangantakarta da kuam yin aiki tare da Iran musammana wadanan bangarori.

Shi ma a nasa bangaren karamin jakadan an Iran a Kampala Mohammad Reza Ghezelsofli ya bayyana cewa, aiki tsakanin Iran da Uganda ba sabon lamarin ba ne, domin kuwa suna dadddiyar alaka a tsakaninsu wadda ba ta taba yankewa ba, wadda kuma kullum kara habaka take yia dukkanin bangarori.

Ya ce Irana shirye take ta yi tare da Uganda a dukkanin bangarori domin al'ummmin kasashen biyu su ci moriyar juna kuma su amfana da wanan kyakkyawar alaka.

Baya ga haka kuma ya ce hala lamarin yake dagane da dukkanin sauran kasashen Afirka, wadanda ya ce ya zama wajibi a yi aiki tare domin amfana da dukaknin kwarewa da kowace kasa take da ita domin amfanin juna, inda ya ce Iran a shirye take domin yin hakan tare da dukkanin kasashen Afirka.

 

4016462

 

 

 

captcha