IQNA

Shugaban Kasar Aljeriya Ya Caccaki Morocco Kan Kulla Yarjejeniyar Tsaro Da Isra'ila

19:36 - November 27, 2021
Lambar Labari: 3486612
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Aljeriya ya nuna rashin jin dadinsa kan yarjejeniyar tsaro da kasar Maroko ta kulla da gwamnatin sahyoniyawan ziyarar da ministan yakin isra’ila ya kai jiya a birnin Rabat.

Shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Taboun ya bayyana takaici  matuka kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Morocco da gwamnatin yahudawan sahyoniyawa a ranar jiya 26 ga watan Disamba.

Teboun ya shaida wa kafar yada labaran kasar cewa "Muna bakin ciki da yadda Maroko ta kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila da nufin  cimma yarjejeniyar ayyukan soji a tsakaninsu."

Shugaban na Aljeriya ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga wani jawabi da ministan harkokin wajen Isra'ila Yair Lapid ya yi a kafafen yada labaran kasar Morocco, inda yake kara jaddada cewa Isra’ila mamba ce mai sanya a  yanzu a kungiar tarayyar Afirka, inda shugaba na Aljeriya ya ce, "Yanzu mun kudiri aniyar kalubalantar matakin shigar da Isra'ila cikin kungiyar Tarayyar Afirka gadan-gadan.

Tun da farko shugaban majalisar dokokin Aljeriya Saleh Qoujil ya bayyana cewa, kasarsa na daya daga cikin kasashen da suke nuna damuwa da takaici da ziyarar da ministan yakin Isra'ila ya kai a kasar Maroko.

Qujil ya ce: "Makiya suna kara samun kayan aiki don su cutar da Aljeriya, A yau lamarin ya kara fitowa fili ga kowa a lokacin da muka ga ministan yakin gwamnatin sahyoniyawan yana ziyarar aiki a wata kasa da ke makwabtaka da Aljeriya.

 

4016438

 

 

captcha