IQNA

Yau Ce Ranar Ranar Duniya Ta Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Falastinu

16:56 - November 29, 2021
Lambar Labari: 3486620
Tehran (IQNA) a yau ne ake gudanar da tarukan ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu ta duniya a majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashe daban-daban.

Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 29 ga Nuwamba a matsayin ranar duniya ta hadin kai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu.

A ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar 1977 Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wannan rana da kuri’u mafi rinjaye, inda ta ayyana ranar a kalandar duniya,  tare da yin kira ga kasashe mambobin majalisar da su sanya wannan rana a cikin kalandarsu da kuma raya ta a kowace shekara.

A wannan karon Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da wani taro na musamman a yau 29 ga watan Nuwamban 202, tare da halartar mambobin majalisar, da kuma shugaban babban zauren majalisar gami da shugaban kwamition tsaro, da kuma babban sakataren majalisar Antonio Guterres.

A cikin kuduri mai lamba 37/60 na ranar 1 ga Disamba 2005, babban taron MDD ya yi kira ga kwamitin kare hakkin al'ummar Palasdinu da gwamnatin Palasdinu da su gudanar da bikin ranar hadin kai da nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu, da gudanar da wani taron al'adu tare da hadin gwiwar gwamnatin Falastinu.

Kungiyoyi na masu fafutuka  akasashen larabawa da na musulmi da ma wasu wadanda ban a musulmi, suna raya wannan rana, ta hanyar gudanar da taruka da kuma yin jawabai dangane da halin da al’ummar Falastinu suke ciki, zalunci da danniya da mamaya da Isra’ila ke yi a kansu da yankunansu.

 

4017013

 

captcha