IQNA

Wani Rahoto Ya Ce Ana Kokarin Halasta Kyamar Musulmi A Nahiyar Turai

19:37 - January 05, 2022
Lambar Labari: 3486783
Tehran (IQNA) wani rahoto ya yi nuni da cewa ana kokarin halasta kyamar musulmi a nahiyar turai.
Rahoton shekara-shekara mai suna "Kyamar Musulunci a Turai" ya nuna yadda ake kokarin halasta kyamar Musulunci da nuna wariya ga Musulmi a kasashen Turai da dama.
 
Cibiyoyin jami'o'i 37 daga kasashe daban-daban ne suka shirya wannan rahoto mai taken "Rahoton Turai kan kyamar Musulunci 2020" mai shafuka 886, Wannan rahoto ya yi nazari ne kan batun kyamar addinin Islama a kasashe 31, musamman a nahiyar Turai.
 
Rahoton ya takaita ayyukan wasu gwamnatocin kasashen Turai na nuna wariya ga musulmi da hankoron wasu ‘yan siyasa masu tsatsauran ra’ayi na halasta kyamar Musulunci.
 
Muhimman matakan da wannan rahoto ya dauka a matsayin yunkurin halasta kyamar Musulunci a kasashen Turai sun hada da wasu matakai da wasu gwamnatocin turai suka dauka, daga ciki har matakin gwamnatin Austria, inda ta samar da taswirar dijital mai suna "National Map of Islam".
 
Wannan taswira na kunshe da jerin sunaye da adireshi na masallatai sama da 620, kungiyoyin musulmi da kuma fitattun jagorin musulmi a kasar, inda wasu masana kan dokoki a turai suka bayyana wannan taswirar ta dijital dake bin bin diddigin lamurran musulmi a Austria a matsayin laifi bisa doka.
 
A Belgium, Kotun Tsarin Mulki a watan Yuli 2020 ta yanke hukuncin dakatar da alamomin siyasa da na addini, musamman hijabi, daga manyan makarantun ilimi na kasar.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4026271
captcha