Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News cewa, Sheikh Al-Azhar Ahmed Al-Tayeb ya zabi Dr. Nahle Al-Saeidi shugaban tsangayar ilimin addinin musulunci a birnin Alkahira a matsayin mai ba shi shawara.
Wannan dai shi ne karon farko da aka zabi mace a matsayin mai ba wa Sheikh Al-Azhar shawara, saboda shekaru da dama da suka gabata an kebe mukaman nasiha ga maza.