IQNA

Gangamin Allawadai Da Kisan ‘Yan Shi’ar Najeriya A New York

19:48 - December 19, 2015
Lambar Labari: 3467065
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da babban gangami a birnin New York na kasar Amurka domin yin Allawadai da kisan kiyashin da sojojin Najeriya suka yi wa ‘yan shi’a a wannan mako.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Press TV cewa, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga da gangami a birnin New York na kasar Amurka domin yin Allawadai da kisan kiyashin da sojojin gwamnatin Najeriya suka yi wa ‘yan shi’a na kasar.

Ali Naqavi daya daga cikin wadanda suka shirya gangamin ya bayyana cewa, abin da suke bukata a halin yanzu shi ne a sako sheikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

Sayyid Iliya daga majalisar muuslmin kasar Amurka, ya bayyana cewa sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar muslunci a Najeriya yana da matukar muhimamnci a kasar da ma nahiyar Afirka baki daya.

Ya ce a halin babu wani malamin addinin mslunci da yake da tasiri a dukkanin kasashen nahiyar Afirka kamar sheikh Zakzaky, domin kuwa tasirinsa bai takaita gay an shia a ba kawai, har ma da yan sunna da kuma kiristoci.

Haka nan kuma ya bayyana mamakinswa matuka kana bin da wannan sabuwar gwamnati ta Najeriya da ake zaton cewa za ta mayar da hankali matuka wajen hada kan al’ummar kasa, yadda ta bage da aikata kisan gilla kan fararen hula.

Sojojin najeriya sun kai farmaki kan Hsainiyar Baqiyatollah a lokacin da ake gudanar da taron addini, inda suka kashe mutane da dama, daga bisani kuma suka kai hari kan gidan sheikh Zakzaky, inda a nan ma ska kashe darruwan mutane tare da kame wasu, da hakan ya hada har shi kansa malamin.

3467004

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha