IQNA

Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Rufe Makarantar Kur’ani A Mauritania

19:53 - December 19, 2015
Lambar Labari: 3467066
Bangaren kas ada kasa, an gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da rufe wata makarantar kur’ani mai tsarki a kasar Mauriyatniya.


Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-siraj cewa, a garin Nema na Mauritaniya an gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da rufe wata makarantar kur’ani mai tsarki mai tsarki.

Wannan jerin gwano ya zo jim kadsan bayan kammala sallar Juma’a  abirnin, inda dubban mutane suka shiga cikin sahu suna masu yin Allawadai da rufe wannan makaranta da mahukuntan kasar suka yi.

Matakin ya zo ne bayan da gwamnati ta yanke shawara rufe makarantar saboda wasu dalilai, wdanda ba su gamsar da al’ummar kasar ba, musamman al’ummar birnin wadanda yaransu ne ke amfana da makamarntar.

Limaman juma’a a koina cikin fadin kasar sun yi Allawadai da wannan mataki da mahukuntan kasar ta Mauritaniya suka dauka, tare da yin kira da su gagaguta bude wannan makaranta domin yara s ci gaba da karatu.

An bayyana Firayi ministan kasar Yahya Wuld Hamadain a matsayin mutumin da ke da alhakin rufe wannan makaranta da a ke koyar da yara karatun kur’ani.

3465712

Abubuwan Da Ya Shafa: mMauritaniya
captcha