IQNA

Ma’aikatar Addinai A Masar Za Ta Tarjama Kur’ani A Cikin Harsuna 10 na Duniya

23:06 - December 20, 2015
Lambar Labari: 3467515
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar za ta dauki nauyin tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harsuna 10 na duniya domin amfani masu magana da su.


Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, yanzu haka, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar za ta dauki nauyin tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harsuna 10 na duniya domin masu amfani masu amfani da wadannan yaruka.

Bayanin ya ce harsunan su ne turanci, faransanci, Jamusanci, Istanbuli, Spain, Russi, China, Swahili, Indonesia, Albania, domin yada su a duniya.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa daga cikin wadannan kur’anai yanzu haka an kammala tarjama biyu na Faransanci da Chanis, kuma ana duba su kafin buga su domin amfani.

Bayan kammala aikin duba su to za a mika su ga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar domin fitar da su.

Ma’aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar ta ce ta yi hakan ne da nufin yada sahihiyar fahimta dangane da addinin muslunci a duniya, da nufin gyara fahimtar masu rashin fahimta  akansa.

Abin tuni dai shi ne an saka tarjamar ta harsunan Faransanci da chanisanci a kan shafukan yanar gizo domin far amfani da su kafin kammala bugunsu.

3467189

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha