IQNA

Daesh Ta Yi Barazana Ga Kasar Saudiyya

23:08 - December 20, 2015
Lambar Labari: 3467516
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ‘yan ta’addan daesh ta yi barazana ga gwamnatin Saudiyya dangane da kawancen da Saudiyya ta kafa da sunan yaki da ta’addanci.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah News cewa, a yau Daesh kungiyar ‘yan ta’addan ta yi barazana ga gwamnatin Saudiyya dangane da kawancen da Saudiyya ta kafa da sunan yaki da ta’addanci a cikin kasashen musulmi da na larabawa.

Bayanin na Daesh ya ce wadanda suke mulki da suke cikin kawancen suna a matsayin Salibiyawa ne kuma za su yake su domin sun dare kan dukiyar musulmi da kasar musulmi.

Kasar saudiyya wadda ita ce kan gaba wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya ta sanar da kfa wani kawance da ta kira na yaki da ta’addanci, wanda ya hada kasashe 34 na larabawa da musulmi.

Wasu daga cikin kasashen da kawancen ya kunsa da suka hada da Indonesia, Lebanon, Pakistan, Irak da kuma Oman, ba su da labarin cewa suna cikin kawancen, sai dai a labarai suka ji.

Shi dai wannan kawance da ya yi kama da wasan kwaikwayo, yana gudana ne a karkashin jagorancin kasar da take daukar nauyin ‘yan ta’adda a koina  acikin fadin duniya domin cimma burinta.

3467255

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha