IQNA

An Rusa Husainiyar Mabiya Tarikar Shi’a A Nigeria Baki Daya

22:53 - December 21, 2015
Lambar Labari: 3467973
Bangaren kasa da kasa, jami’an sojin gwamnatin Najeriya suka kai sun kammala rusa ginin cibiyar Husainiyar yan shia baki daya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, a harin da jami’an sojin gwamnatin Najeriya suka kaddamar kan fararen hula a Zaria sun kammala rusa ginin cibiyar Husainiyar yan shia baki daya tare da mayar da ita fili.

Bayanin y ace wannan mataki ya zo bayan rusa mafi yawan gininta a lokacin da ska kai hari a makon da ya gabata, inda suka kashe mutane masu yawa, amma daga bisani a jiya sun dawo da manyan motocin rusau suka karasa abin da ya rage.

Gwamnan jahar Kaduna ya bayyana cewa an gina wannan wuri ne ba bisa kaida ba, kuma gwamnatinsa daga yanzu ba za ta kara bari a ci gaba da gudanar da wasu taruka na addini ba in ba tare da izininta ba, kamar yadda ya sanar da kwace wurin da aka gina wannan cibiya.

Tsawon shekaru dai ana gudanar da taruka a wannan wuri, amma ba a tayar da wannan Magana ba sai yanzu, duk kuwa da cewa sauran wuraren ibada bas u fskanci irin wannan tuhuma ba.

3467819

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha