IQNA

Koyar Da Dalibai Musulmi Kare Kai A Makarantar George Washington

23:36 - November 12, 2017
Lambar Labari: 3482093
Bangaren kasa da kasa, an fara koyar da dalibai musulmi a makarantar George Washington a birnin Charkeston yadda za su rika kare kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na wvgazettemail cewa, an fara aiwatar da wani shiri na koyar da dalibai musulmi a makarantar George Washington a birnin Charkeston yadda za su rika kare kansu bangaren makarantun sakandare.

Ibtisam Barazi it ace shugaban kwamitin da ke kula da harkokin musulmi a wannan makaranta, ta bayyana cewa za su bayar da muhimnmanci matuka wajen koyar da yara yadda za su kare kansu daga masu zaluntarsu.

Ta kara da cewa dukkanin msuulmi a fadin Amurka suna cikin hadari mata da maza yara da manya, saboda haka dole ne su san hanyoyin da za su bi domin kare kansu daga mahara.

Baya ga haka kuma ta bayyana cewa, ba kare kai ne kawai suke koyar da yaran ba, suna koyar da su yadda za su yi mu'amala da mutane cikin hankali da natsuwa da kuma sani ya kamata, sai dai idan an nemi cutar da su to za su kare kansu.

3662319


captcha