Kamfanin dillancin labaran iqna, Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Abbas Moussavi, ya ce yana da kyau a gudanar da bincike kan ire iren wadannan al’amuran dake faruwa, saboda hakan babbar barazana ce ga sha’anin tsaro da kuma zurga zurga ta jiragen ruwa a yankin Golf.
Iran dai na mai danganta lamarin da yadda wasu kasashe ke kokarin wargaza tsaron kan ruwa.
A jiya ne dai hadaddiyar daular larabawa, ta tabbatar da cewa an kai wasu ayyuka data danganta dana aika-aika kan wasu jiragen ruwa na ‘yan kasuwa a gabashin Fujairah, saidai ba tare da bayyana wadanda suka aikata hakan ba.