Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayan kasar Saudiyya, kasar Indonesia za ta zama kasa ta biyu a duniya da za ta bude dakin ajiye kayan tarihin manzon Allah da addinin mulsunci a kasar.
Bayanin ya ce za a bude wannan dakin kayan tarihi nea garin Depok da ke cikin gundumar Jawa ta yamma, a kusa da babbar jami’ar musulunci da ke yankin.
An sanya hannu kan gina wanann wuri tsakanin kungiyar limaman musulmi na kasar Indonesia, da kuma cibiyar malamai ta duniya a abban ginin kungiyar kasashen musulmi da ke birnin Jidda.
Abin tuni dai shi ne, dakin ajiye kayan tarihin manzon Allah guda daya ne ke akwai a birnin Madina Almunawwara.