IQNA

Zanga-Zangar Falastinawa Kan Kin Amincewa Da Kulla Alaka Da Isra'la

23:20 - September 15, 2020
Lambar Labari: 3485188
Tehran (IQNA) kungoyiyon Falastinawa na gudanar da jerin gwano a yau domin nuna rashin amincewarsu da shirin wasu gwamnatocin larabawa na kulla alaka da Isra’ila.

Rahotanni daga Falastinu na cewa, a yau ana gudanar da gangami a dukkanin birane da kauyuka na Falastinu, domin nuna rashin amincewa da shirin wasu gwamnatocin larabawa na amincewa da Isra’ila a hukumance.

Wannan na zuwa ne bayan da dukkanin kungiyoyin Falastinawa gami da gwamnatin falastinawa suka yi kira a kan hakan, inda ake kona hotunan sarakunan kasashen Bahrain da UAE,a a biranan Quds, Ramallah, Nablus da sauran yankunan zirin Gaza.

A sauran kasashen laravawa daban-daban an gudanar da irin wannan gangami, domin nuan goyon baya ga al’ummar Falastinu, tare da yin tir da sarakunan larabawan da suka mika kai ga yahudawa, tare da bayyana su a matsayin masu cin amanar al’umma.

A yau ne ake rattaba hannu tsakanin Bahrain, UAE da kuma Isra’ila, a fadar White House da ke Amurka, kan yarjejeniyar kulla hulda diflomasiyya tsakaninsu.

3923175

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gangami zanga-zanga
captcha