IQNA

Jagora Ya Halarci Makokin Tunawa Da Ranar Shahadar Imam Ridha (AS)

23:11 - October 17, 2020
Lambar Labari: 3485282
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya halarci makokin tunazawa da ranar shahadar Imam Ridha (AS) .

Hojjatol Islam Abidini shi ne ya gabatar da jawabi, inda ya yi tsokaci kan matsayin limaman ahlul bait (AS) da kuma yadda suka kasance masu wakilci na hakika ga manzon Allah, ta hanyar gaskiyarsu da yawan ibdarsu, sadaukarwarsu, da kuma yadda suke dora al’ummar musulmi kan sahihin tafarki na koyarwar manzon Allah kai tsaye kamar yadda ya gadar musu.

Haka nan kuma Mahmud Karimi ya gabatar karatun makoki tare ambatar kadan daga cikin irin matsaloli da Imam Ridha (AS) ya fuskanta tare da sarakunan lokacinsa da suka yi sanadiyyar yin shahadarsa.

3929660

 

 

 

captcha