IQNA

Ana Samun Karuwar Nuna Kiyayya Ga Musulmi A Faransa

23:17 - October 17, 2020
Lambar Labari: 3485283
Tehran (IQNA) ana samun karuwar nuna kiyayya ga musulmi a cikin kasar Faransa fiye da kowane lokaci a kasar.

Hukumomin Faransa sun ce sun kara kama mutane 5 baya ga wasu 4 da suke a tsare, da ake zargin suna da hannu a kisan da wani mutum ya yi wa malamin makaranta ta hanyar yankan rago ranar jiya Juma’a a birnin Paris.jiya

Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, wani matashi ne mai shekaru 18 dan asalin yankin Checheniya, ya halaka malamin ne a wajen makarantarsa, jim kadan bayan kammala baiwa dalibansa darasi, inda ya nunawa daliban zanen batunci da cin zarafi ga manzon Allah inda shi ma jami’an ‘Yan sanda na kasar suka bude wutar bindiga a kansa, inda shi ma suka kashe shin an take.

Wannan dai ba shi ne karon  farko da wasu ke daukar fansa kan masu zanen batunci da cin zarafin manzon Allah a kasar ta Faransa ba,  wanda ake yi da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi ko kuma fadar albarkacin baki.

A watan Satumban da ya gabata jaridar cherlie hebdo ta sake wallafa zanen batunci da cin zarafin manzon Allah abin da ya fusata wasu musulmi suka sake kaiwa ofishin jaridar farmaki a birnin Paris, inda akalla mutane 4 suka jikkata.

A farkon watan Satumban ne kuma shugaban Faransa ya yi kakkausar suka kan mutanen da ke neman shaidar zama a kasar, amma suke bijirewa wasu daga cikin dokokinta ciki har da ‘yancin cin zarafi da yin batanci a kan abubuwa masu tsarki da wasu suke girmawa, wanda kuma kundin tsarin mulkin Faransa ya bayar da damar yin hakan, abin da su kuma musulmi ba su  amince da shi a kan addininsu ko abubuwa masu tsarki a cikin addininsu ba.

 

3929666

 

 

 

captcha