IQNA

Faransa Na Shirin Korar Musulmin Da Ta Kira Masu Tsatsauran Ra'ayi

22:42 - October 19, 2020
Lambar Labari: 3485290
Tehran (IQNA) Faransa tana shirin korar wasu musulmi da ta kira da masu tsatsauran ra'ayi.

Kamfanin dilalncin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Faransa za ta kori mutane dari biyu da talatin da daya, ‘yan kasashen waje daga kasar, saboda abinda ta kira tsatsauran ra’ayi na mai yiyuwan su aikata ayyukan ta’addanci a kasar.
Gwamnatin kasar ta Faransa ta dauki wannan matakin ne kwanaki biyu, bayan kisan wani malamin makaranta wanda wani matashi mai tsatsauran ra’ayin addinin ya yi a kusa da birnin Paris babban birnin kasar.

a kiyayyan da gwamnatin kasar Faransa ta ke nunawa musulmi a duniya da kuma goyon bayan da take bawa wasu kangiyoyi, da sunan ‘yencin fadin albarkacin bakinsu, su na cin mutuncin mabiya wasu addinai na daga cikin abubuwan da suke tunzura matasa musulman kasashen na Turai yi abin turaida suke yi.

Wannan halin na gwamnatin Faransa da sauran kasashen na tura dai ya sa wasu yan ta’ada su na amfani da makaman hannu kamar wuka don kashe mutane.

3930061

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gwamnatin Faransa
captcha