IQNA

Kungiyoyin Falastinawa Sun Gargadi Saudiyya Kan Yunkurin Kulla Alaka Da Yahudawan Isra'ila

23:14 - November 24, 2020
Lambar Labari: 3485396
Tehran (IQNA) kungiyoyin Falastinawa sun gargadi masarautar Saudiyya kan yunkurin kulla alaka da yahudawan Isra'ila biyo bayan ziyarar Netanyahu a Saudiyya.

Kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa daban-daban sun yi Allah wadai da ziyarar da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kai kasar Saudiyya da kuma ganawa da yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bin Salman, suna masu bayyana hakan a matsayin ha’inci da cin amanar tafarkin Palastinu.

Yayin da ya ke magana kan ziyarar, kakakin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Sami Abu Zuhri, ya bayyana ziyarar a matsayin wani lamari mai hatsarin gaske yana mai kiran mahukutan Saudiyya da su yi wa al’umma bayanin abin da ya faru don kuwa a cewarsa hakan wani cin mutumci ne ga al’ummomi kana kuma yin karen tsaye ne ga hakkokin al’ummar Falastinu.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Jihadi Islami yayi tir da kasar Saudiyya saboda daukan bakuncin Netanyahun tana mai cewa hakan yana iya zama share fagen ci gaba da wuce gona da iri a kan al’ummar Falastinu, al’ummar Musulmi da kuma wurare masu tsarki na Musulunci.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana ziyarar Netanyahun a matsayin cin amanar Falastinu kana kuma ha’inci ga Masallacin Qudus da kuma garuruwan Makka da Madina masu tsarki.

A Litinin ne dai wasu kafafen watsa labaran Isra’ilan suka ba da rahoton cewa firayi ministan Isra’ilan Benjamin Netanyahu tare da shugaban kungiyar leken asirin Isra’ila MOSSAD, Yossi Cohen sun tafi Saudiyyan a asirce inda suka gana da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman da kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo da ke ziyara a lokacin a Saudiyyan.

3937018

 

 

 

captcha