IQNA

Taron Kara wa Juna Sani Na Limaman Masallatai A Kasar Uganda

14:55 - December 19, 2020
Lambar Labari: 3485472
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman taron karawa juna sani na limaman masallatan kasar Uganda tare da halartar wasu daga cikin wakilan kungiyoyin addini.

A rahoton da cibiyar kula da harkokin al’adu da addini ta kasar ta fitar, ta bayyana cewa, a jiya an gudanar da zaman taron karawa juna sani na limaman kasar Uganda tare da halartar wasu daga cikin wakilan kungiyoyin addini a birnin kampala fadar mulkin kasar.

Wannan taro dai ya gudana ne bisa hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkoki a’adu da addinai ta kasar Uganda da kuma takwarata ta kasar Iran, wanda kuma wannan ba shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan zaman taron karawa juna sani ba.

Taron ya samu halartar limamai da malaman addinin muslunci da kuma wakilan wasu kungiyoyi da cibiyoyi na addini, kamar yadda kuma an gayyaci wakilan majami’oi na mabiya addinin kirista.

Wadanda suka gabatar da jawabai sun mayar da hankali kan muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma, da kuma girmama juna tsakanin dukkanin mabiya addinai, wanda kuma dama shi ne abin da addinin muslunci ya koyar.

Gwamnatin kasar Uganda ta yi lale marhabin da hakan, tare da kara nuna cikakken goyon bayanta kan gudanar da irin wadannan taruka, domin hakan ya taimaka wajen kara karfafa dangantaka tsakanin al’umma a cikin rayuwarsu ta zamantakewa.

3941866

 

captcha